Isa ga babban shafi

Duk da tsadar rayuwa, tattalin arzikin Turai ya karu

Tattalin arzikin kasashen dake amfani da kudin Euro ya farfado a watan Afrilu a daidai lokacin da yankin ke ci gaba da fama da tsadar rayuwa ta dalilin hauhawar farashin kayayyakin masarufi.  

Kwamishinan Tattalin Arzikin Tarayyar Turai, Paolo Gentiloni
Kwamishinan Tattalin Arzikin Tarayyar Turai, Paolo Gentiloni © AFP
Talla

Sakamakon wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa, tattalin arzikin ya karu daga kashi 53 zuwa 54 tsakanin watan Maris zuwa Afrilun da muke ciki.  

Wani Babban masanin tattalin arziki a Bankin Kasuwancin Hamburg, ya bayyana cewa alkaluma da ke fitowa daga kasashen ya nuna yadda tattalin arzikin yankin ke farfadowa, sai dai ya yi gargadin cewa akwai bukatar kara maida hankali domin har yanzu bai daidaita ba.

Farfadowar tattalin arzikin na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen ke fama da matsin rayuwa ta dalilin hauhawar-hauhawar farashin kayayyakin masarufi.

Duk da raguwar hauhawar-hauhawar da kusan kashi 7 a watan Maris, amma har yanzu ya zarce kashi biyu cikin ɗari da Babban Bankin Turai ke kokarin ya koma. 

Ko da yake damuwa game da koma bayan tattalin arzikin na nahiyar Turai ya dan ragu a baya-bayan nan, wani jami'in Asusun Ba da Lamuni na Duniya ya yi gargadin cewa Turai za ta fuskanci koma baya sossai na ci gaban tattalin arziki a bana. 

Kasar Jamus wadda ita ce kasa daya tilo da hasashen Asusun Bada Lamuni ya nuna za ta fada cikin karayar tattalirziki a bana, hakan ya biyo bayan tasiri da yakin Ukraine da Rasha ya yin ne a kanta.  

Bayanan sun kuma nuna cewa, an samu raguwar kayayayyakin da masana’antun Faransa ke fitarwa.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.