Rasha ta tabbatar da mutuwar fararen hula 21 a harin da Ukraine ta kai
Ma'aikatar kula da ayyukan agaji ta Rasha ta ce akalla mutane 21 ne suka mutu a wani kazamin harin bam da Ukraine ta kai birnin Belgorod a jiya asabar, daga cikin su akwai kananan yara 3, sannan wasu 111 suka jikkata.
Wallafawa ranar:
Cikin sanarwar da Ma'aikatar tsaron Rashar ta fitar, ta ce ba za ta bari kashe mutanen da Ukraine ta aikata mata ya tafi a banza ba, inda ta kara da cewa gwamnatin Ukraine din na kakokarin karkata hankula ne daga lallasasu da ta ke yi a fagen daga.
Bayan kai harin, Rasha ta bukaci ta gudanar da taron gaggauwa da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya dan tattauna harin, kamar yadda wakilinta a majalisar, Dmitry Polyanskiy ya sanar.
Harin na ranar Asabar na zuwa ne bayan makamancin shi da Rasha ta kai wa Ukraine a daren alhamis zuwa safiyar ranar juma'a, hari mafi girma da Kasar ta taba kai wa tun bayan mamayarta a Ukraine da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 40, wasu 150 kuma suka jikkata.
Hukumomin Ukraine ba su amince da zargin kai haren cikin Rasha ba ko kuma a yankin Crimea, tun bayan da Moscow ta kwace ikon wasu daga cikin yankunanta a shekarar 2014.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu