Isa ga babban shafi
FIFA

Platini ya kare zargin da ake ma shi

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai Michel Platini yace yana cike da farinciki kuma fafutikar da ya k e yi ba wai ta kashin kansa ba ne illa ganin ci gaban kwallon kafa a duniya.

FIFA ta dakatar da Sepp Blatter da Michel Platini na tsawon shekaru 8
FIFA ta dakatar da Sepp Blatter da Michel Platini na tsawon shekaru 8 AFP
Talla

Platini ya fadi haka ne bayan ya gurfana gaban kwamitin daukaka kara a jiya a hedikwatar FIFA a Zurich.

Platini ya ce yanzu zai zira ido ya ji sakamakon hukuncin da FIFA za ta yanke bayan ya daukaka karar.

A yau Talata ne Sepp Blatter tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA zai gurfana gaban kwamitin domin kalubalantar dakatar da shi na shekaru 8 daga sha’anin kwallon kafa.

A watan Disemba ne dai kwamitin da’a na FIFA ya dakatar da Platini shugaban hukumar kwallon Turai da kuma Sepp Blatter na tsawon shekaru 8 kan badakalar kudi dala miliyan biyu da ta shafi shugabannin biyu na kwallon kafa.

Ana zargin Platini ne da karbar kudaden daga Blatter, akan wani aikin kwagila da ya yi.

Amma Platini yace da ya san shi mai laifi ne da ya gudu. Wannan ne kuma ya haramtawa ma shi shiga takarar neman kujerar shugabancin hukumar FIFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.