Isa ga babban shafi
Wasanni

Har yanzu akwai sauran aiki a gabanmu - Messi

Gwarzon dan wasan Barcelona Lionel Messi ya ce, nasarar da suka samu kan Liverpool a zagayen farko na wasan kusa da na karshe a gasar zakarun Turai da kwallaye 3-0, ba ya nufin suna da tabbacin kaiwa wasan karshe.

Lionel Messi.
Lionel Messi. REUTERS/Albert Gea
Talla

A cewar Messi, ya so adadin kwallayen da suka jefa ya kai 4, amma duk da haka, abin alfahari nasarar da suka samu, sai dai ya bukaci su zage damtse a mako mai kamawa, idan suka yi tattaki zuwa Ingila don sake karawa da Liverpool a filin wasa na Anfield.

Messi ne dai ya zura kwallaye 2, yayin da Suarez ya ya jefa guda.

Zalika kwallaye biyun da Messi ya jefa a ragar Liverpool jiya, sun sa adadin kwallayen da ya ci wa kungiyarsa ta Barcelona kaiwa 600 a jimlace.

Tuni dai mai horar da kungiyar Liverpool Jurgen Klopp ya ce ba shakka ya amince cewar, ba za su iya dakile bajintar dan wasan Barcelona Lionel Messi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.