Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

PSG na shirin sauya matsaya kan sayar da Neymar

Rahotanni daga Faransa na nuni da cewa, kungiyar kwallon kafa ta PSG ba ta niyyar sayar da Neymar Junior cikin wannan Kakar musayar ‘yan wasan duk kuwa da yadda dan wasan ya zaku da sauya sheka, haka zalika shima tsohon Club din na sa ya nuna bukatar dawo da dan wasan.

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG Neymar Junior
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG Neymar Junior REUTERS/Ricardo Moraes
Talla

Neymar dan Brazil mai shekaru 27 da kan sa ne ya zabi komawa Barcelona bayan da PSG ta mika tayin musayarsa da Paul Pogba na Manchester United, wanda shi ma ya zaku don sauya sheka zuwa Real Madrid.

A shekarar 2017 ne dai Neymar ya sauya sheka daga Barcelonar ta Spain zuwa PSG a Faransa, kan tsabar kudi yuro miliyan 198, inda kuma tun a bara ya fara kokarin sauya sheka daga PSG amma sai a wannan karon ne ya fito karara ya nuna bukatar tafiyarsa har ma da barazar kauracewa doka tamaula matukar ba a gaggauta kammala cinikinsa ba.

Sai dai tsohon manajan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, kuma mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a yanzu, Pep Guardiola ya ce baya tunanin komawar Neymar Barcelona ce tafi dacewa da shi a yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.