Isa ga babban shafi
FARANSA-GASAR OLYMPIC

Yau ake kaddamar da soma zagayen belin wutar gasar Olympic ta duniya.

Bayan share tsawon watanni ana ta fadi tashi, a yau juma’a ne,  komitin shirya wasannin gasar Olympic na 2024 a birnin Paris a yau juma’a ne  ya ke fitar da jadawalin zagayen belar wutar gasar olympique a kasashen duniya, wanda hakan ke  kasancewa  hutu,   bayan binciken da aka gudanar,  da ya shafa kashin kaji ga mutuncin gasar ta Olympique, al’amarin da ya kamata a ce  ya wakana ne bayan gudanar da shagulgulan gasar mai zuwa.

Ibrahim Al-Hussein ya karbi belar wutar olympique daga hannun shugaban komitin shirya gasar ta  olympique, Spyros Capralos.
Ibrahim Al-Hussein ya karbi belar wutar olympique daga hannun shugaban komitin shirya gasar ta olympique, Spyros Capralos. REUTERS/Alkis Konstantinidis
Talla

Sai dai kotun ta yi watsi da bukatar yin hakan da komitin tsare tsaren ya gabatar, wanda bada jimawa ba ya fice daga badakalar  tsadar  tikitin shiga gasar ta Olympque, da wasu ke cewa ya yi yawa.

A ranar talatar da ta gabata, a harabar ofisoshin komitin shirya gasar, da kamfanin  Solideo ke kula da tafiyar da muhiman ayuka gasar,  sun fuskanci binciken daga jami’an ofishin alkali mai binciken kudi Faransa (PNF) sakamakon wasu ayuka da suka kasance abin zargi da komitocinbiyu  suka gudanar.

Kotu dai ta maida hankali ne,  kan wasu kwangiloli da aka bayar a karkashin gasar ta Olympique.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.