Mai rabo ne zai samu tikitin kallon gasar Olympics a Paris
An sake fitar da tikiti dubu 400 na kallon wasannin Olympics da za a ci gaba da siyarwa a karshen watan Nuwamba, karkashin gasar da birnin Paris na kasar Faransa zai karbi bakunci a shekarar 2024.
Wallafawa ranar:
Masu shirya gasar, sun ce tikiti miliyan 10 ake sa ran za a sayar a wasannin da za su gudana daga ranar 16 ga watan Yuli, zuwa 11 ga Agusta.
Shugaban shirya gasar, Michael Aloisio, ya ce ya tikiti miliyan bakwai da 200,000 aka siyar ya zuwa yanzu.
“Ba na tunanin akwai wani kwamitin da ya taba daukar nauyin wannan gasa da suka taba sayar da adadin tikici mai yawa cikin kankanin lokaci kamar na Faransa,” in ji Aloisio.
Ana ta cece-kuce kan yadda aka sanya farashin wasu daga cikin tikitin da ake siyarwa a birnin Paris, la’akari da cewa ana siyar da wasu akan farashin Yuro 50, inda a wasu wuraren kuma bah aka abin yake ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu