Isa ga babban shafi

Faransa na neman ma'aikata fiye da dubu 16 da zasu yi aiki yayin gasar Olympics

Kwamitin shirya wassanin Olympic na birnin Paris, ya shiga kiciniyar neman cike gurbin ma’aikata dubu 16 da zasu yi aiki a yayin gasar,  kama daga kan  masu wanke- wanke  direbobin motoci, masu dafa abinci da kuma injiniyoyi. 

Faransa ta fara shirye-shiryen karbar bakuncin gasar cikin lokaci don gudun kaucewa samun matsala.
Faransa ta fara shirye-shiryen karbar bakuncin gasar cikin lokaci don gudun kaucewa samun matsala. AP - Michel Euler
Talla

Daga mako mai zuwa ne za a kaddamar da fara daukar ma’aikatan a garin wasannin Olympic dake unguwar Saint-Dinis ta birnin Paris,  inda masu bukata za su hallara, don fara tantance kwarewar su, aikin da ke zuwa watanni 10 kafin fara gudanar da gasar ta 2024.

Wannan dai na zuwa ne yayin da aka kasa daukar ma’aikata a wasu fannoni  masu matukar muhimmanci na gasar ta Olympic sanadiyar  barkewar annobar cutar Covid- 19,  wannan yekuwar daukar ma’aikata masu yawa  a karkashin gasar ta Olympic zai zama kalubale  a bangaren masu aikin gadi masu zaman kansu, da kuma na masu dafa abinci  a cewar   Cecile Martin ta ofishin ministan ayyuka ta kasar.

Daya daga cikin yankunan da za a gudanar da gasar Olympics na Paris ,Seine-Saint-Denis.
Daya daga cikin yankunan da za a gudanar da gasar Olympics na Paris ,Seine-Saint-Denis. © ©SOLIDEO – Dronepress.

Sai dai kuma wata  matsalar ita ce ayar dokar gwamnati kan yan ci rani, da aka shirya kadawa kuri’a a watan Nuwamba mai zuwa,  da ta dora sharadin cewa sai masu katin izinin neman  aiki a wasu fannonin ilimi, za a dauka aiki, abinda zai iya haifar da tarnaki wajen  cike gibin ma’aikatan da ake bukata. 

Hakan dai na nufin cewa,  daga mako mai zuwa mutanen da suka taba yin irin wannan aiki na Olympic ne zasu fara zama kan gaba wajen sake basu wannan dama fiye da sabbin shiga. 

Kamfanin da zai kula da ciyar da  yan wasan a sansanoni 14 na bukatar daukar ma’aikata akalla dubu 6. 

A yayin da Kamfanin da zai kula da sufuri na faransa RATP,  ke bukatar daukar dirbobin jigilar yan wasa,  sai kuma fannin tsaro da ke bukatar daukar masu gadi da yawansu ya kama daga dubu 17 zuwa dubu 22 domin tabbatar da ganin gasar ta Olympique ta gudana cikin nasara. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.