Isa ga babban shafi
UN

MDD ta nemi kasashen duniya da su tashi tsaye game da batun sauyin yanayi

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, dole ne kasashen duniya su dauki muhimman matakai domin tunkarar matsalolin da sauyin yanayi ke haifar wa duniya.

Zubar dusar kankara a kasar Rasha
Zubar dusar kankara a kasar Rasha REUTERS/Alexander Demianchuk
Talla

‘’Muna rayuwa ne a cikin wani yanayi na kalubale da duniya ke fuskantar manyan matsaloli da sauyin yanayi ke haifarwa’’, a cewar Jan Ellianson mataimakin babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya da ke gabatar da jawabi ga mahalarta taron kasa da kasa.

Wani rahoton da Majalisar ta fitar a cikin makon da ya gabata mai magana kan dabarun rage kaifin illolin wannan matsala ta sauyin yanayi na cewa, tuni duniya ta yi asarar dalar Amurka miliyan dubu biyu da miliyan dari biyar a cikin shekaru goma na wannan karni sakamakon sauyin yanayi.

Rahoton ya ce mummunar asarar da aka samu cikin wadannan shekaru, lamari ne da ke matukar tayar da hankula, domin kuwa alkalumman sun wuce hasashen masana nesa ba kusa.

Hukumar dai ta yi gargadin cewa, dole ne kasashen duniya su dauki matakai domin tunkarar matsalolin da ke tare matsalar ta sauyin yanayi, tare da bayar da misalin abubuwan da suka taba faruwa a baya irinsu ambaliya, mahaukaciyar guguguwa da dai sauransu, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane masu tarin yawa a sassan duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.