Isa ga babban shafi
Turai

Serbia ta sayo alluran Corona daga China

Kasar Serbia da ta soma yiwa yan kasar ta allurar rigakafin cutar Coronavirus a lokutan sallar krismeti shekarar da ta shude ta karbo a yau asabar alluraran rigakafin cutar corona kimanin milyan daya daga China.

An soma yiwa mutane allurar rigakafin cutar coronavirus a Serbia
An soma yiwa mutane allurar rigakafin cutar coronavirus a Serbia Reuters
Talla

Tun ranar 24 ga watan Disemban 2020 ne Serbia kasa mai yawan al’uma milyan 7 ta kasance kasa ta uku da ta soma yiwa mutan kasar wannan allura,bayan kasashen Birtaniya da Rasha.

A jimilce mutane kusan 20.500 kama daga jami’an kiwon lafiya, gajiyayu na kasar ne suka amfana da alluran farko a kasar ta Serbia.

Indan aka yi tuni ranar 30 ga watan Disemba na shekarar 2020 ne wani kamfanin kasar China mai suna Sinophram ya sanar da gano wata allura da ingancin ta zai kai kashi 79 cikin dari wajen yakar cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.