Isa ga babban shafi
Najeriya

Yawan wadanda suka rasa rayukansu a sansanin Rann da ke Kalabalge ya karu

Yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hari bisa kuskure da jirgin yakin Najeriya ya kai kan sansanin ‘yan gudun Hijira na Rann da ke karamar hukumar Kalabalge ta jihar Borno ya karu zuwa 236.

Sansanin 'yan gudun hijira na Rann da ke Borno da mayakan Boko Haram sukai yunkurin kai hari
Sansanin 'yan gudun hijira na Rann da ke Borno da mayakan Boko Haram sukai yunkurin kai hari Médecins sans Frontières (MSF) / AFP
Talla

Shugaban karamar hukumar ta Kalabalge Babagana Malaria ya bayyana alkalumman, yayin da yake wa babban Hafsan rundunar Sojan kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, karin haske kan yadda hadarin ya auku, wanda ya kai ziyarar gani da ido zuwa sansanin ‘yan gudun hijirar.

Laftanar Janar Buratai ya nemi afuwar mutanen yankin, tare da bukatar kada gwiwarsu tai sanyi game da kokarin da sojin Najeriya suke yi na kare su.

A cewar Babban hafsan Sojan, mayakan Boko Haram da suka yi yunkurin kawowa sansanin hari suka yi niyyar tarwatsawa da fari, kafin a samu kuskuren aukawa fararen hular, sai dai ya bayyana jin dadinsa bisa yadda sojin Najeriyar suka fatattaki mayakan tare da kashe 15 da motarsu guda da suka kwace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.