Isa ga babban shafi
Najeriya

Tallafin dala biliyan $1 ya yi kadan - Rundunar sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce dala biliyan daya da gwamnati ke bukatar a ware don yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabashin kasar sun yi kadan matuka.

Shugaban sashin rundunar sojin Najeriya ta ‘Operation Lafiya Dole’ da ke yakar ta’addancin Boko Haram, Manjo Janar Rodgers Nicholas.
Shugaban sashin rundunar sojin Najeriya ta ‘Operation Lafiya Dole’ da ke yakar ta’addancin Boko Haram, Manjo Janar Rodgers Nicholas. Daily Nigerian
Talla

Bayanin ya zo ne yayin da sojojin Najeriya ke ci gaba da samun nasarori a yakin suke yi na murkushe ragowar mayakan Boko Haram a yankin na arewa maso gabashin kasar.

Shugaban sashin rundunar sojin kasar ta ‘Operation Lafiya Dole’ da ke yakar ta’addancin Boko Haram, Manjo Janar Rodgers Nicholas ne ya bayyana haka, yayin da yake yi wa manema labarai Karin bayani kan ayyukan jami’ansa a jihar Borno.

Manjo Janar Nicholas ya bada misalin cewa, jirgin yakin nan na zamani kirar Super Tucano da gwamnatin tarayya zata saya daga Amurka, kowanne daya kudinsa yana kai wa dala miliyan $14.

Shi kuwa jirgin yaki mai saukar ungulu, kirar zamani da rundunar sojin ke son saya, kudinsa yana kamawa daga dala miliyan $20 zuwa dala miliyan $65 kowanne daya.

Dangane da batun ajiye makaman mayakan Boko Haram kuwa, Manjo Janar Nicholas ya ce da dama daga cikin su na son mika makamansu, sai dai tsoro yana hana su hakan, to sai dai Nicholas ya jaddada cewa babu wanda sojoji zasu kashe ko su ci zarafinsa daga cikin mayakan, muddin suka mika makamansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.