Isa ga babban shafi
Najeriya

Borno: 'Yan gudun hijira 2000 sun koma muhallansu a Guzamala

Rundunar sojin Najeriya ta ce a karon farko cikin shekaru 6, kimanin ‘yan gudun hijira 2000 sun koma muhallansu da ke garin Gudumbali a karamar hukumar Guzamala da ke jihar Borno, inda suka yi bukukuwan Salla.

Jami'in sojin Najeriya tare da wasu 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, a wani sansani da ke garin Maiduguri, a jihar Borno.
Jami'in sojin Najeriya tare da wasu 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, a wani sansani da ke garin Maiduguri, a jihar Borno. AFP/STRINGER
Talla

Shekaru 6 da suka gabata ilahirin mazauna karin na Gudumbali ne suka tsere, sakamakon yawaitar hare-haren da mayakan Boko Haram ke kai musu.

Sanarwar Daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Texas Chukwu, ya ce ‘yan gudun hijirar sun samu komawa garin nasu ne, sakamakon nasarorin da suka samu wajen murkushe mayakan Boko Haram.

Daraktan yada labaran ya kara da cewa, nan gaba kadan, sojin Najeriya, zasu sake bude wasu karin garuruwan, da ke kananan hukumomi tara a arewacin jihar Borno.

Birgediya Janar Texas ya bada tabbacin cewa zasu ci gaba da tabbatar da tsaro ga ‘yan gudun hijirar, kuma gwamnati za ta taimaka musu wajen sake gina muhallan da rikicin Boko Haram ya lalata.

Sugum Mele, shi ne kwamisinan ma'aikatar kasa da sifiyo na jihar Borno wanda shi ma dan garin na Guzamala ne yayi wa wakilinmu Bilyaminu Yusuf karin bayani.

00:58

Sugum Mele kan komawar 'Yan gudun hijira 2000 muhallansu a Guzamala

Bilyaminu Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.