rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Faransa Emmanuel Macron Lagos Al'adu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaba Macron ya ziyarci gidan Fela da ke Legas

media
Shugaba Emmanuel Macron da Angélique Kidjo da gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode Youssou N'Dour na Senegal a gidan rawar Fela REUTERS / Akintunde Akinleye

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci gidan rawa na New Afrika Shrine da shahararren mawakin Najeriya, Fela Kuti ya assasa a unguwar Ikeja da ke birnin Leags, gidan rawar da ya shahara saboda rakashewa da kuma zuke-zuken tabar wiwi.


Kuti ya bude sabon gidan rawar ne don maye makamancinsa da mahaifisa, marigayi Fela Anikulapo Kuti ya assasa kafin a kona a shekarar 1977.

Femi Kuti da dan uwansa Seun Kuti sun ci gaba da raya al’adun gargajiyar da mahaifinsu ya dora su akai gabanin mutuwarsa, yayin da suka gaje shi a fannin salon waka da kida na Afrobeat.

A yayin gabatar da jawabi a gidan rawar, shugaba Macron ya ce, Najeriya na nada matukar muhimanci ta fuskar raya al’adun nahiyar Afrika,

Shugaban ya ce, Faransa na shirin kaddamar da wasu jerin shirye-shirye don yada al’adun Afrika a nahiyar Turai.

Marigayi Fela ya shahara sosai a duniya musamman a Afrika saboda wasu dabi’u da ya kebantu da su da suka hada da nuna tsaraici da shaye-shayen wiwi da kuma caccakar gwamnatin soji na wancan lokaci.

Shugaba Macron ya ziyarci gidan rawar ne bayan ganawarsa da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a birnin Abuja, in da suka tattauna kan matsalar tsaro da tattalin arziki.