Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta kori tuhumar da ake yiwa mabiya akidar Shi’a 35

Wani Alkali a birnin Abuja dake Najeriya yayi watsi da tuhumar aikata laifukan tayar da tarzoma da ake yiwa wasu mabiya akidar Shi’a 35 daga cikin daruruwan da aka kama bayan arangama da ‘Yan Sanda.

Wasu jami'an 'Yan Sandan Najeriya, yayin tarwatsa taron mabiya akidar Shi'a.  30/10/2018.
Wasu jami'an 'Yan Sandan Najeriya, yayin tarwatsa taron mabiya akidar Shi'a. 30/10/2018. REUTERS/Abraham Achirga
Talla

Mai shari’a Musa Ibrahim ya amince da bukatar lauyan dake kare wadanda ake zargin na watsi da karar saboda rashin bayyanar lauyan dake gabatar da karar a kotun.

Sauran wadanda ake zargin da suka ki amincewa da tuhumar da ake musu, sun samu beli kan sharadodi daban daban.

Akalla mabiya Shi’a 120 ake zargi da tada hankali a birnin na Abuja, a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar neman gwamnati ta saki jagoransu, Ibrahim El Zakzaky daga tsrewar da ta yi masa tun a shekarar 2015, sakamakon arrangamar da magoya bayansa suka yi da sojoji a garin Zaria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.