Isa ga babban shafi
Najeriya

NAPTIP za ta ceto 'yan matan Najeriya dubu 20 daga Mali

Hukumar yakar cin zarafi da safarar dan adam ta Najeriya NAPTIP, ta ce shirinta yayi nisa na kokarin ceto kimanin ‘yan matan kasar dubu 20, da akai safararsu zuwa Mali.

Wasu daga cikin 'yan matan Najeriya da suka fada hannun masu safarar mutane.
Wasu daga cikin 'yan matan Najeriya da suka fada hannun masu safarar mutane. Reuters
Talla

Yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran kasar NAN a Abuja, darakatar hukumar ta NAPTIP, Mis Julie Okah-Donli, ta ce an yi safarar ‘yan matan ne zuwa sassan Mali, domin yin karuwanci.

Mis Okah-Donli ta ce, sun gano halin da ‘yan matan na Najeriya ke ciki, hadi da adadinsu, bayan binciken da wasu jami’an hukumar ta NAPTIP suka yi, yayin ziyarar sirri da suka kai kasar ta Mali, a watan Disambar bara.

Daraktar ta NAPTIP ta kara da cewa mafi akasarin ‘yan matan da aka yi safarar ta su, an yaudaresu ne da cewa za’a kaisu kasar Malaysia domin aiki a Otal-Otal da gidajen abinci.

Wasu ‘yan matan kuma a cewar hukumar yaki da safarar dan adam din ta Najeriya, an kaisu kasar ta Mali cikin kayan makaranta, lamarin da ke nuna cewa an sace su ne ta karfi, akan hanyarsu ta zuwa ko dawowa daga karatu.

Binciken hukumar ta NAPTIP ya kuma gano an sayar da wasu ‘yan matan akan naira dubu 600, inda ake yin lalata da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.