Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta soki bayyanar gwamnonin Nijar a yakin neman zaben Buhari

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta soki shugaban kasar Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC, kan bayyanar wasu gwamnonin jihohin Jamhuriyar Nijar a yakin neman zaben shugaban da ya gudana a birnin Kano.

Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Uche Secondus tare da dan takarar jam'iyyar a zaben shugabancin Najeriya Atiku Abubakar.
Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Uche Secondus tare da dan takarar jam'iyyar a zaben shugabancin Najeriya Atiku Abubakar. Daily Post Nigeria
Talla

A ranar Alhamis 31 ga Janairu, Gwamnan Jihar Zinder, Issa Amoussa da na Jihar Maradi, Zakari Umaru suka bayyana a jihar Kano, sanye da babbar rigar da aka yi wa kwalliya da zanen kwado da linzami mai dauke da tambarin Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, domin taya shugaban kasar Muhammdu Buhari yakin neman zabe.

Sai dai yayin mayar da martani kan yakin neman zaben, shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus, ya bayyana zargin cewa APC na shirin yin fasakaurin dubban ‘yan jamhuriyar Nijar domin kada mata kuri’a a zaben shugaban kasa da ke tafe a ranar 16 ga watan Fabarairu.

A cewar Secondus idan ba wata makarkashiya aka kulla ba, me zai sanya wasu gwamnoni daga Nijar su bayyana a yakin neman zaben shugabancin Najeriya?

Shugaban na PDP ya kara da cewa, lamarin ya nuna alamun jam’iyyar APC ta dade tana hayar ‘yan Jamhuriyar Nijar domin halartar gangamin yakin neman zabukanta da ke gudana.

Sai dai a gefe guda, duk da cewa, ba kasafai aka saba ganin haka a Najeriya ba, wasu masharhanta sun ce, babu wata dokar zabe karara da ta haramta wa wasu ‘yan kasashen ketare taimaka wa wani dan siyasar kasar wajen yakin neman zabe.

A farkon watan Disambar bara, Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta musanta zargin da aka yi mata, na dauko hayar dubban mutane daga Jamhuriyar Nijar, domin halartar taron kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kasar dan takararta Atiku Abubakar a Sokoto.

PDP ta maida martanin a waccan lokacin ne ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa’i, wanda yayi zargin cewa, PDP ta dauko hayar mutane daga Nijar ne domin nuna cewa tana da tarin magoya fiye da tunani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.