rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Najeriya Amurka APC PDP

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta musanta fifita wani bangare a zaben Najeriya

media
Jakadan Amurka a Najeriya Stuart Symington. YouTube

Kasar Amurka ta musanta zargin cewa tana goyan bayan wani bangare a zaben Najeriya da za’ayi a karshen wannan mako, inda ta ce fatanta shi ne ganin an gudanar da karbaben zabe cikin kwanciyar hankali.


Jakadan Amurka a Najeriya Stuart Symington ya ce sun gamsu da yadda hukumar zabe ke gudanar da ayyukan ta, kuma zaben na Najeriya yana da matukar muhimmanci ga jakadun kasashen duniya kamar yadda yake ga al’ummar kasar.

Jakadan yace Amurka na baiwa Najeriya tallafin sama da Dala biliyan guda kowacce shekara wajen ceto rayukan mutane sama da miliyan biyu ta hanyar kula da lafiya da kuma agaji, inda yake cewa wannan ba zai canja ba saboda muhimancin kasar a matsayin kawar Amurka.

Amurka tace wannan zabe na da matukar muhimmanci ga Najeriya da makotan ta da kuma kasashen duniya saboda rawar da kasar ke takawa a Yankin da kuma Afirka wajen dorewar dimokiradiya.

Sanarwar tace ingancin zaben shekarar 2015 ya daga darajar Najeriya kuma Amurka na fatan sake ganin haka a wannan mako.