Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta yi tur da kutsen Amurka kan al'amuranta

Jam’iyyar APC da ke mulkin Najeriya ta bayyana damuwa kan katsalandan daga Amurka da wasu kasashen duniya kan shirin zaben kasar da zai gudana a karshen wannan mako.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP/Bertrand Guay
Talla

Sanarwar da Daraktan yada labaran Jam’iyyar ta APC Festus Keyamo ya rabawa manema labarai, ta bayyana damuwa kan sukar da kasashen ke yi wa shirin zaben da kuma dakatar da babban mai shari’a Walter Onnoghen daga kujerar sa.

Keyamo yace wadannan kalamai za su iya jefa shakku kan shirin zaben da kuma aiwatar da shi, inda yake cewa babu wanda zai shiga Najeriya ya bayyanawa kasar yadda za ta tafiyar da harkokin ta, kamar yadda su kansu kasashen ba za su yadda da irin kutsen ba.

A karshen watan Janairun da ya gabata, Kungiyar Tarayyar Turai, Amurka da Birtaniya sun bayyana damuwa kan matakin na dakatar da Onnoghen, wanda ake zargi da kin bayyana wasu makudan kudaden kasar waje da ya mallaka a asusunsa, kamar yadda dokar da’ar ma’aikata a Najeriya ta tanada.

Kungiyar tarayyar Turai EU, kira tayi ga gwamnatin Najeriya da kuma ‘yan adawa, su bi tsarin doka, wajen warware takaddamar da matakin dakatar da Alkalin Alkalan ya haifar.

A nata bangaren, Amurka ta ce ta damu da matakin ne, la’akari da cewa, an sauya alkalin alkalan, ba tare da hadin gwiwar bangaren majalisar dokokin kasar ba. Yayinda Birtaniya ta ce matakin zai iya shafar sahihancin zabukan kasar na 2019 da za’a yi nan da makwanni kalilan, inda tace bai kamata a dauki matakin a irin lokacin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.