Isa ga babban shafi
Najeriya

"Za mu durkusar da arzikin Najeriya muddin Buhari ya lashe zabe"

‘Yan tawayen Niger Delta sun yi barazanar durkusar da tattalin arzikin Najeriya muddin aka sake zaben shugaba Muhammadu Buhari a wa’adi na biyu a zaben 2019.

Wasu daga cikin 'yan tawayen Niger Delta da ke kudancin Najeriya
Wasu daga cikin 'yan tawayen Niger Delta da ke kudancin Najeriya AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

‘Yan tawayen sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Alhamis, kasa da sa’oi’i 42 a gudanar da zaben shugabancin kasar.

‘Yan tawayen sun ce, suna fatan kawo karshen mulkin Buhari ta hanyar zabar babban mai adawa da shi na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da suka ce suna goyon baya.

Mayakan Niger Delta Avengers sun taka rawa a wasu rikice-rikicen da suka taimaka wa wajen tsindimar Najeriya cikin matsalar koma-bayan tattalin arziki a shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.