rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Sokoto

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana farautar 'yan bindigar da suka sace dan majalisa a Sokoto

media
Garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa na addabar wasu jihohn arewacin Najeriya Jakarta Globe

Jami’an ‘yan sandan jihar Sokoto da ke Najeriya na fararutar wasu ‘yan bindiga da suka sace daya daga cikin mambobin Majalisar Dokokin Jihar mai wakiltar mazabar Denge/Shuni, wato Hon. Aminu Magaji.


Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan sandan, ASP Muhammad Sadiq Abubakar ya tabbatar da sace dan majalisar.

ASP Sadiq ya ce, sun samu bayanan da ke cewa, wasu ‘yan bindiga da yawansu ya kai 10, sun kutsa cikin kauyen Bodai da ke Karamar Hukumar Denge Shuni a cikin daren da ya gabata, inda suka sace dan Majalisar.

Jami’in ya ce, ‘yan sandan na gudanar da farautarsu a dazuka da zummar ceto dan majalisar tare kuma da cafke ‘yan bindigar.

Garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa na ci gaba da addabar wasu jihohin arewacin Najeriya, kodayake, jami’an tsaron kasar na aiki tukuru don ganin sun kawo karshen mataslar.