Boko Haram ta kunshi kabilu da dama sabanin lokutan baya - Zulum
Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, Babagana Umara-Zulum, ya ce a halin yanzu, mutane daga kabilun kasar da dama ne ke cikin kungiyar Boko Haram, sabanin kabila guda da a baya ake danganta su da kungiyar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwamnan na Borno ya shaidawa manema labarai haka ne a wannan asabar, bayan ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Abuja.
Umara Zulum ya kuma ce muddin ana son gaggauta kawo karshen matsalar Boko Haram, tilas dauki matakan warware matsalolin da suka haifar da tayarda kayar bayan, da kuma batutuwan da suke karfafa kungiyar ta Boko Haram.
Gwamnan ya kara da jaddada bukatar kara yawan jami’an tsaro a kauyukan dake jihar Borno, da kuma girke dakarun a inda babu su a baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu