rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Bauchi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mai-dakin marigayi Tafawa Balewa ta rasu

media
Marigayiya Jummai Abubakar Tafawa Balewa. The Nation

Mai dakin Fira Ministan farko na Najeriya marigayi Abubakar Tafawa Balewa da ta rage a raye, Hajiya Jummai Tafawa Balewa, ta mutu tana da shekaru 85.


Hajiya Jummai rasu ne a birnin Legas, kwanaki kalilan bayan dawowa daga kasar India, inda ta yi jinyar ciwon zuciya.

Wata majiya daga iyalan tsohon Fira Ministan ta ce, marigayiyar ta tsaya a Leags ne bayan dawowa daga India kafin daga bisani ta koma Bauchi.

Majiyar ta kara da cewa, Hajiya Jummai Tafawa Balewa ta rasu ne da safiyar ranar lahadin nan bayan dogon suman da ta yi, sakamakon bugawar da zuciyar ta tayi.