rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shirin dakatar da manyan ma'aikata zuwa kasashen waje neman lafiya a Nijar.

media
Jerin Mata masu shayarwa a Nijar suna jiran Likita RFI-HAUSA

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana shirin dakatar da manyan ma’aikatan ta tafiya kasashen waje domin kula da lafiyar su.

Jamhuriyar Nijar na  daga cikin kasashen da tattalin arzikin su ke da rauni,wanda kuma hakan zai tilastawa Gwamantin kasar inganta bangaren kiwon lafiya cikin dan karamin lokaci.


Ministan lafiya Dr Ilyasu Idi Mainasara ya ce an dauki matakin ne domin rage makudan kudaden da gwamnatin kasar ke kashewa kowacce shekara.

Da jimawa kungiyoyi masu zaman kansu sun koka ganin ta yada manyan ma'aikatan kasar ke yawan tafiya kasashen waje wajen domin kula da lafiyar su yayinda wasu yankunan kasar ke fama da karancin asibitoci.

Ministan lafiya ya jadada cewa yin haka zai taimakawa sosai wajen ceto tattalin arzikin kasar.