Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa zata sake nazari kan salon aikin Jami'an tsaronta

Ana cigaba da samun arrangama tsakanin mutanen gari da ‘yansanda a kasar Faransa, bayanda a kwanakin baya, aka zargi wani jami’in tsaro, da yiwa wani matashi bakar fata fyade da kulki.

Arrangama tsakanin wasu 'yan Faransa da jami'an tsaro sakamakon cin zarafin matashi bakar fata,Théo.
Arrangama tsakanin wasu 'yan Faransa da jami'an tsaro sakamakon cin zarafin matashi bakar fata,Théo. Gregoire HOZAN / AFP
Talla

Shugaba Francois Holland, ya bukaci ‘yan kasar da su kwantar da hankulansu, tare da cewa doka za ta yi aiki kan jami’an da suka aikata wannan laifi, tare da yi wa aikin tsaro a kasar garambawul.

Holland ya sha wannan alwashi ne yayinda ya kai ziyara asibitin da aka kwantar da matashi Thoe mai shekaru 22 bayan cin zarafin da akai masa.

Wannan al’amari dai ya janyo yamutsi a sassan kasar Faransa, tsawon kwanaki 7, wanda ya kai ga kamen mutane da dama da suka kona motoci da kuma fasa shaguna.

Tuni dai aka gurfanar da Jami’in dan sandan da yaci zarafin matashi Thoe bisa laifin aikata fyade yayinda aka gurfanar da sauran jami’ani 3 da laifin cin zarafin dan’adam.

Zalika ministan cikin gida na Faransa, Bruno Le Roux, ya tabbatar da dakatar da jami’an ‘yan sandan 4 daga aiki domin tauna tsakuwa don aya taji tsoro.

Le Roux ya kara da cewa nan bada dadewa ba, za’a dauki matakan sauya tsarin kame da kuma gudanar da tambayoyi da jami’an tsaron Faransa ke wa wadanda ake zargi da aikata laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.