Isa ga babban shafi
Mexico

Sake Motsawar kasa ya dakatar ayyukan ceto a Mexico

Sake motsawar kasa, ya dakatar da yunkurin jami’an agaji a Mexico, na ceto wadanda aukuwar girgizar kasa ta biyu a kasar ta rutsa da su.

Jami'an ceto a Mexico yayinda suke bincika karkashin gine-ginen da girgizar kasa ta rusa a birnin Mexico City.
Jami'an ceto a Mexico yayinda suke bincika karkashin gine-ginen da girgizar kasa ta rusa a birnin Mexico City. REUTERS/Henry Romero
Talla

Cibiyar bincike kan girgizar kasa ta Amurka ta ce karfin motsawar kasar da ya sake aukuwa a garin Matias Romero, ya kai maki 6.1, yayinda zurfinsa ya kai kilomita tara cikin karkashin kasa.

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasar Mexico ta ce, motsawar kasar, ya samo ragowa ne daga girgizar kasar da tayi sanadin mutuwar sama da mutane 305 a ranar Talatar da ta gabata, mai karfin maki 8.1.

Fatan gano Karin wadanda suke raye a karkashin gine-ginen da suka rubza na cigaba da dusashewa, bayan aukuwar girgizar karo na biyu, a ranar da al’ummar kasar ke bikin cika shekaru 32 da aukuwar girzizar kasar da tayi sanadin mutuwar dubban mutane a shekarar 1985.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.