Kasuwar baje kolin jiragen yaki na kasashen Duniya a Faransa
A Faransa, yau litinin aka bude babbar kasuwar baje kolin jirage dake gudana a birnin Paris, motoci da sauran kayayyakin tsaro mafi girma a duniya da ake kira Eurosatory.
Wallafawa ranar:
A bana, kamfanonin kera makamai dubu daya da 750 ne ke halartar kasuwar baje kolin daga kasashen duniya 63 a wani yanayi da duniya ke fama da manyan kalubale ta fannin tsaro.
Stéphane Mayer, shi ne shugaban kamfanin kera kayan yaki da ake kira Nexter a Faransa wanda ya hada guiwa da KMW na Jamus a 2015,ya kuma bayyana cewa duk wata kasa a duniya, Faransa ce ko kuma Amurka, na fatan saka makudan kudade a bangaren tsaro musamman lura da halin da duniya ke ciki a yau, sakamakon yadda kasashe suka shiga yanayi na gasa da juna a wannan fanni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu