Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

A shirye mu ke mu karawa Birtaniya lokacin fita - EU

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta ce a shirye ta ke ta bai wa Birtaniya cikakkiyar damar jinkirta ficewar ta daga kungiyar har zuwa wa’adin da aka gindaya na ranar 29 ga wannan wata.

Shugaban Majalisar Kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk tare da jagoran shirin ficewar Birtaniya daga EU Michel Barnier
Shugaban Majalisar Kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk tare da jagoran shirin ficewar Birtaniya daga EU Michel Barnier OLIVIER HOSLET / POOL / AFP
Talla

Shugabannin kungiyar na fatar ganin Firaminista Theresa May ta halarci taron da za su yi ranar alhamis da wani shirin ficewa domin amincewa da shi kafin ranar 29 ga wata.

Kungiyar ta ce idan Birtaniya na bukatar karin lokaci ta na iya bayyanawa kafin cikar wa’adin ranar da aka gindaya.

A makon jiya ne dai Majalisar Birtaniya ta kada kuri'ar karshe da ta yi watsi da yarjejeniyar da Theresa May ta kulla da EU, sai dai kuma a bangare guda majalisar ta yi watsi da batun sake kada kuri'a kan shirin ficewar kasar daga EU.

A hukumance dai kwanaki 11 yanzu ya ragewa Birtaniya ta fice daga kungiyar ta EU kamar yadda aka yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu ta kunsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.