Isa ga babban shafi
Wasanni

Wassar Tennis da gyaran Hillaye da kuma rugbuy

A wassar Tennis ta Wimbledon da ke gudana a kasar Ingla, bangaren mata, ‘yar kasar Czech Petra Kvitova ta kai karo na karshe ,bayan ta lashe yar kasar Belarus Victoria Azarenka, da ci 6-1, 3-6, 6-2. Za a soma sukuwar basukur ta zagayen France , wato Tour de France, daga ranar 2 ga watan gobe zuwa ranar 24 ga watan na Yully.wanan shi ne karo na 98.Sukuwar na da matakai guda 21 da su ke da tazarar kilomita dubu 3 da 430. A wassar cin koffin kwallon zari-ruga ta duniya, wato Rugbuy ta wanan shekara ta 2011 da za ta gudana a kasar New Zealand,a yanzu haka dai ‘yan wassar kasar France na cikin yanayin motsa jiki tukuru, kamar yadda ya kamata ,wanan kuma domin su kassance cikin kyaukyawar shiri, kuzari da kwazo. A yanzu dai ta tabata tabat, kanfanin zuba jari ta fanin wassani na kasar Qatar, wato Qatar Sport Investments ya sayi hannun jari a cikin kungiyar wassar kwallon kafa ta Paris Saint Germain ta kasar France da ya kai kishi 70 cikin 100.Sebastien Bazin shugaban wani kanfani da ake kira Colony Capital Europe tsohon kanfanin da ya hi babban jari a cikin kungiyar ta Paris Saint Germain shi ne ya sanar da hakan a yau.Milyon 10 na kudin Yiro ne gwamnatin kasar France ta kebe domin gyara Parc des Princes wani wurin shakatawa na alforma kamar yadda ministan wassani da motsa jiki Chantal Jouanno ta sanar.Wanan kudi su na cikin milyon 158 na yiro da aka kebe domingyara hillayen wassa 11 a France sabo da wassar wassanin kasashen tarrayar turai a shekara ta 2016.  

Wimbledon
Wimbledon
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.