rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Faransa Portugal Poland Gasar Cin Kofin Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Portugal ta tsallaka gaba a gasar Euro 2016

media
Cristiano Ronaldo na Portugal na neman lashe wa kasarsa gasar cin kofin kasashen Turai a bana REUTERS/Darren Staples

Dan wasan Portugal Christiano Ronaldo ya kara samun kwarin gwiwa dangane da fafutukarsa ta neman lashe wa kasarsa kofin gasar kasashen Turai da ake yi a Faransa.


Wannan kuma na faruwa ne bayan Portugal ta samu nasara akan Poland a bugun fanafreti 5-3 a wasan da suka buga a jiya a Marseille, lamarin da ya bai wa Portugal damar tsallaka wa matakin wasan dab da na karshe a gasar ta Euro 2016, yayin da Poland ta fice daga gasar.

Kafin aje ga bugun fanariti sai da kasashen biyu suka buga 1-1 kuma Poland ce ta fara zura kwallo ta hannun Robert Lewandowski a mintina na biyu da fara wasan amma daga bisani Portugal ta farke ta hannun Renato Sanches.

Yanzu haka dai Portugal za ta hadu da Wales ko kuma Belgium.

In anjima ne kasashen Wales da Belgium din za su fafata da juna a matakin wasan dab da na karshe, yayin da kocin tawagar Wales, Chris Coleman ya bayyana cewa, karawarsu ta yau, ita ce mafi muhimmanci a gare su tun lokacin gasar cin kofin duniya wadda aka gudanar a shekara ta 1958.

Kasar dai ba ta taba samun gurbi a matakin wasan karshe na wata babbar gasa ba, tun lokacin da Brazil ta doke ta shekaru 58 da suka gabata a gasar cin kofin duniya.