rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Brazil Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Har yanzu Neymar yana da sauran abin yi a PSG"

media
Dan wasan PSG Neymar, a lokacin da yake kan hanyar isa asibiti domin yi masa tiyata a kafa, sakamakon raunin da ya samu. REUTERS

Mahaifin dan wasa mafi tsada a duniya na PSG, Neymar, ya ce dan sa yana da damar kai wa ga nasarar da yake nema a kungiyar tasa ta PSG, kuma tuni ma ya fara samun nasarorin da yake bukata.


Neymar Santos ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a gidansu da ke jihar Sao Paulo, a Brazil, a lokacin da shugaban kungiyar PSG Nasser Al-Khelaifi ya kai masa ziyara don duba lafiyar dan sa Neymar da ke murmurewa daga raunin da ya samu a kafa, a ranar 25 ga watan Fabarairu da ya wuce.

Kalaman na Mahaifin Neymar sun zo ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da tofa albarkacin baki akan labaran da suke nuni da cewa, dan wasan ya fara kokarin yi wa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona kome, idan kuma hakan ya gagara, tuni mahaifin nasa ya fara tuntubar Real Madrid, dangane da sauyin shekar dan wasan.

A halin da ake ciki, likitoci sun tabbatar da cewa sai neymar ya shafe akalla watanni biyu da rabi zuwa uku, kafin ya warke sarai ya kuma dawo filin wasa.