Isa ga babban shafi
wasanni

An fasa hancin Messi a Old Trafford

An fasa hancin dan wasan Barcelona Lionel Messi a gumurzur da suka doke Manchester United da ci 1-0 a matakin wasan dab da na kusan karshe a Gasar Zakarun Turai, yayinda a gefe guda kumatunsa ya kumbura.

Lionel Messi a Old Trafford
Lionel Messi a Old Trafford reuters
Talla

Chris Smalling da ke tsaren bayan Manchester United ne, ya kai wa Messi hari har ya samu raunin, kuma mawuyaci ne dan wasan ya buga wasan da Barcelona za ta yi da Huesca a ranar Asabar.

Kocin Barcelona, Ernesto Valverde ya ce, tabbas Messi bai jin dadi.

Yanzu haka akwai gagarumin kalubale a gaban Manchester United domin kuwa tana fuskatar barazanar ficewa daga Gasar ta Zakarun Turai, ganin cewa, abu ne mai wahala ta doke Barcelona a karawar da za su sake yi zagaye na biyu a Camp Nou a makon gobe.

Kodayake kocinta, Ole Gunnar Solskjaer na fatan yi wa Barcelona abinda suka yi wa PSG wadda a wasansu na farko ta sha gabansu, amma a zagaye na biyu Manhester United ta yi mata fintinkau.

Sai dai kum, abin luara ana shi ne, sau daya tal aka doke Barcelona daga cikin wasanni 52 da ta karbi bakwacin a gidanta, wato Camp Nou. Kazalika tun shekarar 2013 raban da a samu nasara a kanta a wata fafatawa da ta yi a gidanta nata a Gasar Zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.