Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Liverpool ta samu tsaikon zuwa zagaye na gaba a gasar zakarun Turai

Masu rike da kambun gasar zakarun nahiyar Turai Liverpool za su bukaci maki daya a wasan karshe na matakin rukuni tsakaninsu da Red Bull Salsburg kafin su tsallaka zuwa matakin kungiyoyi 16, bayan canjaras da suka yi da Napoli.

Jurgen Klopp, kocin Liverpool ta Ingila.
Jurgen Klopp, kocin Liverpool ta Ingila. Phil Noble/Reuters
Talla

Saura kiris Liverpool su samu zuwa wannan mataki na zagaye na biyu ta wurin kasancewa kan gaba a rukunin E, amma a tsakiyar wasa kafin hutun rabin Dries Mertens ya yi musu lalata ya jefa kwallo a ragarsu.

‘Yan wasan Liverpool dai ba su tabuka abin kirki ba a zubin farko na wasan, saboda sun kauce wa alkiblar irin wasan da suka saba takawa, sai dai saura kiris da sun saka kwallo ana daf da tafiya hutu ta wurin James Milner amma abin ya ci tura.

Ana cikin gwabzawa ne, har ma sai da aka kai minti na 65, Dejan Lovren ya farke wa masu masaukin bakin kwallon da ta makalle a ragarsu, inda ya saka bugun kusurwa da aka kawo da kai ; nan ne fa filin wasan ya buge da sowa, ‘yan wasan Liverpool suka yi ta gurnani kamar wasu zakuna amma ba su cimma gaci ba

Amma duk da wannan yunkuri na Liverpool, ‘yan wasan Napoli sun daure bayan su tamau, shi ya sa kwallo ta kasa shiga.

Wannan na nufin dole sai ‘yan wasan Liverpool sun samu maki daya a wasan su da Red Bull Salsburg a ranar 10 ga watan Disamba kafin su haye, abin nufi, suna bukatar canjaras, ko kuma su yi addua’r Napoli ta sha kashi a gidan Genk.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.