Isa ga babban shafi
Wasanni

Wane ne gwarzo tsakanin Mane da Salah da Mahrez?

Yau ne za a gudanar da bikin karrama gwarzon dan kwallon Afrika a kasar Masar, yayin da tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger ya yi amanna cewa, zaratan ‘yan wasan Liverpool, wato Mohamed Salah da Sadio Mane ne ke kan gaba wajen lashe wannan kyauta. Wenger na ganin Salah da Mane sun sha gaban Riyad Mahrez na Manchester City.

Mahrez da Salah da Mane
Mahrez da Salah da Mane inews
Talla

Dukkanin ‘yan wasan uku sun nuna bajinta a shekarar 2019, inda Salah da Mane suka lashe kofuna da suka hada da kofin gasar zakarun Turai da UEFA Super Cup da kuma kofin zakarun kungiyoyin nahiyoyin duniya .

Shi kuma Mahrez ya taimaka wa kungiyarsa ta Manchester City sake lashe gasar firimiyar ingila, yayin da ya taimaka wa kasarsa ta Algeria lashe gasar cin kofin Afrika a karon farko cikin shekaru 29, inda suka doke Senegal wadda Mane ke taka mata leda.

Sai dai duk da wannan bajinta ta Mahrez, Wenger na ganin cewa, Salah da Mane sun sha gabansa,  sannan hankalin zai fi karkata a kan su a yayin wannan biki na mika kyautar gwarzon dan wasan na Afrika a Masar.

A ra’ayin Wenger, ya kamata zaratan biyu su raba kyautar a tsakaninsu muddin hakan zai surantu.

A bangaren mata kuwa, ‘yar wasan Najeriya, Asisat Oshola za ta fafata da takwarorinta na Afrika ta Kudu da kuma Kamaru, wato, Thembi Kgatlana da Ajara Nchout.

Oshola wadda ke taka leda a Barcelona ta Spain, ta lashe wannan kyauta a shekarar 2014 da 2016 da kuma 2017, yayin da ake ganin za ta iya sake lashe kyautar a bana.

Su ma matasan ‘yan wasan Super Eagles ta Najeriya, wato Samuel Chukwueze da Victor Osimhen za su fafata da Achraf Hakimi na Morocco wajen lashe kyautar gwarzon matashin dan wasan Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.