Isa ga babban shafi

Wasan Super Eagles da Cape Verde ba mai sauki ba ne-Rohr

Mai horar da kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles, Gernot Rohr ya koka da yadda tawagar kasar ta fito a rukuni guda da Cape Verde karkashin jadawalin hukumar FIFA na wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2022.

Mai horar da kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles Gernot Rohr tare da wasu 'yan wasa.
Mai horar da kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles Gernot Rohr tare da wasu 'yan wasa. AFP PHOTO/Ian KINGTON
Talla

Manajan na tawagar Najeriyar dan Jamus ya bayyana cewa ba abu ne mai sauki ga Super Eagles ta iya doke tawagar Tubaroes Azuis ta Cape Verde ba, tawagar da Eagles din bata taba nasara kanta a wasannin da suka doka a tarhi ba.

Sau biyu Super Eagles ta taba karawa da Cape Verde a tarihi, inda jaririyar kasar ta yi canjaras da Najeriyar yayin wasannin sada zumunta tsakaninsu a 2013, haka zalika tawagar ta lallasa Eagles wadda ke da tarihin dage kofin zakarun Afrika sau 3, yayin wasannin cin kofin WAFU a 2019, a wasan da aka tashi babu kwallo ko guda amma kuma a bugun daga kai sai mai tsaron raga, kasar ta lallasa Najeriyar.

Sauran kasashen da tawagar ta Super Eagles za ta kara da su a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniyar, akwai Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Liberia a rukunin C.

Gernot Rohr tawagarsa ta kasance kasar Afrika ta farko da ta samu tikitin makamanciyar gasar wancan lokaci zuwa Rasha, ya bayyana tawagar ta Cape Verde da Rui Aguas tsohon dan wasan gaba na Portugal da ya taka leda a Benfica da Porto ke jagoranta a matsayin tawaga mafi hadari a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.