rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali ECOWAS CEDEAO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugabannin kasashen Afrika ta Yamma sun yi watsi da ziyarar kasar Mali

media
Reuters/David Lewis

Shugabannin kasashen Afrika ta Yamma, sun yi watsi da shirin ganawa da sabbin mahukuntan mulkin sojan kasar Mali. Rahotanni sun ce masu zanga zanga dake goyon bayan juyin mulkin da Capt Amadou Sanogo, ya jagoranta, sun mamaye filin saukan jiragen saman Bamako babban birnin kasar.

Wani jami’i dake tafiya tare da Shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara, daya daga cikin shugabannin, ya tabbatar da fasa sauka a filin saukan jiragen saman Mali, inda Shugabannin shida, suka koma birnin Abidjan.


Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS-CEDEAO, ta dakatar da kasar ta Mali, kuma ta nemi shugabannin su shiga tsakani, an kuma saka rindinar sojan yankin cikin shirin ko ta kwana.

Yanzu dai za a gudanar da zama kan kasar ta Mali a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire, wadda ke shugabancin kungiyar.

Masu zanga zangar kasar ta Mali na daukan matakin kasashen duniya kan saba ‘yancin kasar.

Cikin makon jiya sojoji suka kifar da gwamnatin farar hular kasar ana shirin gudanar da zabe a watan gobe, yayin da Hambararren Shugaba Amadou Topumani Toure ke shirin kammala wa’adinsa na biyu, bayan shafe shekaru 10 kan madafun ikon kasra dake yankkin yammacin Afrika.