Isa ga babban shafi
Kenya

Kotun Kenya ta yi watsi da bukatar rufe sansanin Dadaab

Wata kotu a kasar Kenya ta yi watsi da bukatar gwamnatin kasar ta rufe sansanin Dadaab na ‘yan gudun hijra, mafi girma a Duniya.

sansanin yan gudun hijirar Somaliya  na Dadaab a kasar kenya
sansanin yan gudun hijirar Somaliya na Dadaab a kasar kenya
Talla

Alkalin kotun, John Mativo, ya ce rufe sansanin ya sabawa dokokin kasa kuma hakan na a matsayin tauye ‘yancin ‘yan gudun hijrar.

Sansanin Dadaab, wanda ya kasance sansanin ‘yan gudun hijra mafi girma a duniya, yana dauke da mutane fiye da dubu dari biyu da hamsin, yawancinsu kuma ‘yan asalin Somaliya ne da yakin basasa ya tilastawa tserewa daga kasar.

A baya gwamnatin kasar Kenya ta bukaci a rufe sansanin, domin a cewarta mayakan EL-Shabab suna amfani da shi wajen tsara hare-haren ta’addanci, da kungiyar ke kaiwa kasar, da ma kasashen da ke makwabtaka da ita.

Kenya ta zargi mayakan El Shabab na Somaliya da kitsa harin ta’addanci da aka kai a kasuwar zamani ta Westgate da ke Nairobi a shekara ta 2013, da kuma wanda aka kai a jami’ar Garissa a shekara ta 2015, mutane fiye da dari ne suka mutu a hare-haren guda biyu.

A watan Satumbar shkerar da ta gabata, hukumar kare hakkin ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tilastawa ‘yan gudun hijrar Somalia komawa kasarsu, ya sabawa dokokin duniya, ganin halin kunci da za su iya samun kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.