rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Morocco Kungiyar Kasashen Larabawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Yan Sanda A Morocco Sun Dambace Da Masu Zanga-Zanga

media
Sarkin Morocco Muhammad na shida RFI

Jami'an tsaro a kasar Morocco sun kara da masu zanga-zanga a yankin Al-Hoceima kwana daya bayan da Sarkin kasar Mohammed na shida ya soki jinkirin da ake samu na ayyukan ci gaba a yankin.


Bayanai na nuna masu zanga-zangan sun tare hanyoyi yayin da ‘yan sanda suka yi kokarin fasa taron da karfin tsiya.

Majiyoyi na cewa masu boren sun fito ne daga garuruwan makwabta da suka hada da Imzouren da Tammassin.

Tun watan goma na shekarar data gabata ake samun yawaitan zanga-zanga a yankin Al-Hoceima mai tashan jiragen ruwa amma kuma ya kasance mafi koma baya ta fannin ci gaba a gunduman Rif.