rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An rufe daya daga cikin manyan jami’o'in Kenya

media
Daya daga cikin manyan jami’oi da ke kasar Kenya AFP PHOTO / CARL DE SOUZA

An rufe daya daga cikin manyan jami’oi da ke kasar Kenya, sakamakon zanga-zangar da ya barke tsakanin dandazon ‘yan adawa da ke birnin Nairobi kan zaben shugabancin kasar da aka gudanar.


Daraktan da ke kula da harkokin dalibai, John Orindi ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, jami’an kasar sun tilasta wa daliban jami’ar Nairobi da su yi gaggawan barin dakunan kwanan su, sakamakon rikicin da ya barke.

A cewar daraktan da ke kula da harkokin dalibai, john Orindi, sun rufe jami’ar ne saboda umarnin da suka samu daga hukumar gudanarwar makarantar.

Tun a cikin satin da ya gabata aka soma zanga-zangar wanda ke biyo bayan tsare Babu Owino, tsohon shugaban daliban, wanda ba da dadewa ba ya yi nasarar samun kujerar majalisa, kana yana a matsayin babban mai goyon bayan dan adawan gwamnatin kasar Raila Odinga.

A ranar 26 ga watan Oktober da muke ciki ake saran za a sake fafatawa tsakanin shugaba mai ci Uhuru Kenyatta da abokin hamayyarsa Raila Odinga bayan Kotun Koli ta soke zaben farko da aka gudanar a cikin watan Agusta saboda kura-kuren da ta ce an samu.

A yanzu haka dai, Odinga na bukatar gwamnatin kasar ta kori wasu daga cikin manyan jami’an hukumar zaben kasar da aka zarga da tafka magudi a zaben shugabancin kasar da aka gudanar.