Isa ga babban shafi
Afirka

An damke masu safarar mutane a yammacin Afirka

Hukumar ‘yansandan kasa-da-kasa (INTERPOL) ta ce an damke masu safarar mutane guda 40 tare da ceto mutane 500 a wani samame a yammacin nahiyar Afirka.

Mutane da dama kan fada kangin bauta yayin da suke kokarin tsallakawa zuwa Turai.
Mutane da dama kan fada kangin bauta yayin da suke kokarin tsallakawa zuwa Turai. MAHMUD TURKIA / AFP
Talla

Hukumar ta kai wannan samame ne a lokacin da kasashen duniya ke kokawa game da cinikin bayi da aka bankado a kasar Libya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, INTERPOL ta ce akwai kananan yara guda 236 daga cikin mutane dari biyar da aka ceto.

Hukumar ta kara da cewa samamen ya gudana ne a kasashen Chadi, da Mali, da Mauritania, da Niger, da kuma Senegal.

Za a gabatar da mutanen da aka damke din a gaban kotu bisa zargin su da laifuka da suka hada da safarar mutane, da tursasa yin bauta, da kuma bautar da kananan yara, in ji INTERPOL.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.