rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali Nijar Mauritania Algeria Sahel Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masu jihadi sun nuna hoton bidiyon Sophie Petronin

media
Hodon Sophie Pétronin da masu ikirarin jihadi suka yada © AFP

Shafin yanar gizon wata kungiya da ta kira kanta Jama’at Nasrat Al-Islam Wal Muslimin, ya nuna hoton bidiyon Sophie Petronin, wata jami’ar agaji ‘yar kasar Faransa da aka ‘yan bindiga suka sace a watan disambar shekara ta 2016 a garin Gao da ke arewacin Mali.


A cikin hoton bidiyon, ma’aikaciyar agajin mai shekaru 72 a duniya, ta roki mahukuntan Faransa da su taimaka domin ceto rayuwarta daga hannun ‘yan bindigar.

Sau da dama shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, na yin alkawarin cewa za a ceto wannan mata, da ta share tsawon shekaru tana ayyukan jinkai cikin kasar ta Mali.