Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan gudun hijira daga Rann na kwarara zuwa kasar Kamaru

Hukumar Kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mazauna Rann 30,000 suka tserewa gidajen su daga Rann dake Jihar Borno domin samun mafaka a kasar Kamaru, bayan harin kungiyar boko haram.

Yan gudun hijra a yankin Gamboru dake jihar Borno
Yan gudun hijra a yankin Gamboru dake jihar Borno REUTERS
Talla

Kakakin hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Babar Baloch yace hukumar ta shaidawa taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva cewar, matakin ya biyo bayan janyewar sojojin Kamaru wadanda suke aiki a karkashin rundunar hadin kai ta kasashe 4 dake yaki da Boko haram a yankin.

Gwamnan Lardin Arewa mai nisa a Kamaru, Mijinyawa Bakary yayi zargin cerwar sojojin Najeriya sun fice daga garin, shi yasa mazaunan sa neman mafaka a kasar su.

Bakary ya musanta zargin cewar sun hana yan gudun hijirar shiga kasar su, inda yake cewa kofa a bude take domin karbar su, kuma suna tattaunawa da hukumomin agaji na Najeriya da Kamaru domin taimakawa bakin.

Sai dai kakakin sojin Najeriya, Janar Sani Usman Kukasheka a wata sanarwa yace har yanzu sojojin Najeriya na garin Rann.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.