rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Algeria Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 183 sun jikkata a zanga-zangar Algeria

media
Masu zanga-zangar adawa da tazarcen shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika, yayin arrangama da 'yan sanda a birnin Algiers. 1/03/2019. REUTERS/Ramzi Boudina

Ma’aikatar lafiya ta Algeria, ta ce mutane 183 sun jikkata a zanga-zangar da dubban ‘yan kasar ke ci gaba da yi, ta adawa da tazarcen shugaba AbdelAziz Bouteflika da ke neman wa’adi na 5.


Tun a makon da ya gabata aka soma zanga-zangar a sassan kasar musamman a birnin Algiers, amma a ranar Juma’a ta yi karfi, lamarin da ya haifar da arrangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar da ke kokarin kutsawa harabar fadar gwamnatin kasar.

Zanga-zangar dai ita ce mafi girma da aka taba yi a Algeria cikin shekaru 8, bayan kadawar guguwar sauyi a kasashen Larabawa.

Bouteflika ya dare mulkin Algeria a shekarar 1999 zuwa yanzu, sai dai tun a 2013, ya daina fita bainar jama’a, bayan kamuwa da ciwon mutuwar barin jiki.