Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta janye jakadanta daga Afrika ta Kudu

Najeriya ta janye jakadanta da ke Afirika ta Kudu, Kabir Bala yayinda ta kuma fice daga taron tattalin arzikin duniya da aka fara gudanarwa a birnin Cape Town a wannan Laraba saboda hare-haren da ake kai wa ‘yan kasarta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Kamfanin Dillancin Labaran Kasar, NAN ya ce, gwamnatin Najeriya ta kuma bukaci biyan diyya kan ‘yan kasarta da aka kashe, sannan aka kwashe dukiyoyinsu a hare-haren kyamar baki a Afrika ta Kudu.

Najeriya ta dauki matakin janye jakadanta ne a wani taro da ya samu halartar shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama a fadar gwamnatin kasar da ke birnin Abuja.

Tuni kasashen Congo da Rwanda da Malawi, su ma suka janye daga taron tattalin arziki na duniya na kwanaki uku da aka fara gudanarwa a Afrika ta Kudun saboda wannan farmakin na kyamar baki a kasar.

A yayin bude taron na tattalin arziki, shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya ce, suna fuskantar babban kalubale kan yadda wasu mutane ke daukar doka a hannunsu, yana mai sukar hare-haren kyamar baki a kasarsa.

A bangare guda, gwamnatin Najeriya ta jibge jami’an tsaro kan kadarorin Afrika ta Kudu da ke kasar sakamakon yunkurin matasan kasar na kai wa kadarorin harin ramuwar gayya, yayinda aka rufe katafaren shagunan Shoprite da ofisoshin sadarwar MTN mallakan Afrika ta Kudun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.