Isa ga babban shafi
Afrika ta kudu-Najeriya

Ramaphosa ya yi tir da hare-hare kan baki a Afrika ta kudu

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya yi tir da hare-haren kyamar bakin da ke faruwa a kasar wadda ta kai ga arangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar kin jinin bakin tare da sanadin mutuwar mutane 2.

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa REUTERS/Rodger Bosch
Talla

Cikin kwanakin baya-bayan nan akalla mutane 10 suka mutu sanadiyyar makamantan hare-haren kan baki da kadarorinsu da ke Afrika ta kudu galibi ‘yan Najeriya.

Cikin sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar a yau Laraba ta ce shugaban ya yi tir da matakin kyamar bakin musamman game da abin da ya faru a ranar Lahadin da ta gabata.

Hare-hare kan bakin da kadarorinsu ya tilasta ‘yan Najeriya yunkurin daukar matakin ramuwa musamman kan kadarorin ‘yan Afrika ta kudu da ke kasar, matakin da ya tilasta kulle Ofishin jakadancin Johannesburg da ke Abuja da Lagos.

Haka zalika tuni gwamnatin Najeriya ta yi tayin kwashe al’ummarta da ke son dawowa gida daga Afrika ta kudun inda yanzu haka mutane dari 6 suka yi rijistar tahowa yayinda za a fara jigilarsu daga yau Laraba.

A cewar jakadan Najeriya a Johannesburg, Godwin Adamu za a fara jigilar ‘yan Najeriyar da mutane 320 da za a dakko a yau Laraba.

Akwai dai ‘yan Najeriya fiye da dubu dari da ke zaune a sassan kasar ta Afrika ta kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.