rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan bindigar da suka sace dalibai mata a Kaduna, sun sake su

media
Nigeria: Kaduna-Abuja expressway The Guardian Nigeria

Rahotanni daga Najeriya sun ce yan bindigar da suka sace dalibai mata guda 6 a wata makarantar Sakandare dake Jihar Kaduna, sun sake su bayan karbar diyyar naira miliyan 10.


Jaridar Premium Times da ake bugawaa Najeriya tace an saki daliban Makarantar ‘Engravers College’ ne yammacin jiya juma’a, inda daga bisani aka kai su ofishin yan Sanda da kuma asibiti domin duba lafiyar su.

Arewacin Najeriya ya kazanta da lamuran  garkuwa da jama'a,a dai-dai lokacin da jama'a ke ci gaba da kokawa da rashin cikkaken tsaro a yankunan su.

Wasu daga cikin iyayen yaran da suka ga ‘yayan su sun tabbatar da labarin.