Isa ga babban shafi
Afrika

Mutane da dama sun mutu a Madagascar

Ruwan sama masu karfin gaske a Madagascar sun haddasa mutuwar mutane 26,yayinda wasu mutane 15 ruwa suka yi awon gaba da su.Iftila’in ya tilastawa mutane dubu 90 rasa matsugunin su a cewar hukumar dake da kula da hatsura ta kasar.

Daya daga cikin unguwanin 'Antananarivo a kasar Madagascar
Daya daga cikin unguwanin 'Antananarivo a kasar Madagascar MAMYRAEL / AFP
Talla

Iftala’in ya fi muni ne a yankin arewa maso gabacin kasar inda aka bayyana datsewar hanyoyin zuwa wadannan wurare.

Firaministan kasar Christian Ntsay ya bayyana lamarin a matsayin babbar asara ga kasar Madagascar, ya kuma yi amfani da wannan dama tareda yi kira zuwa manyan kasashe don ganin sun kawo dauki zuwa kasar Madagascar.

Gwamnati ta girke jami;an tsaro a wasu yankunan domin dafawa kungiyoyin agaji wajen kai dauki ga jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.