Isa ga babban shafi
Syria

Turkiya ta tabbatar da guba a harin Syria

Sakamakon binciken harin da ya hallaka mutane fiye da 80 a Syria ya nuna cewa, an yi amfani da makami mai guba wajen kai kazamin farmakin a garin Khan Sheikhoun da ke lardin Idlib, kamar yadda ministan shari’a na kasar Turkiya, Bekir Bozdag ya sanar.

Daya daga cikin kwararrun kiwon lafiya na Turkiya a yayin duba wani da harin Syria ya shafa
Daya daga cikin kwararrun kiwon lafiya na Turkiya a yayin duba wani da harin Syria ya shafa Ferhat Dervisoglu/Dogan News Agency/REUTERS
Talla

Kimanin fararen hula 32 ne da harin ya shafa aka kai su Turkiya, in da mutane uku daga cikinsu suka mutu, abin da ya sa kwararru suka yi gwaji kan gawarwakinsu, in da suka gano cewa an yi amfani da makami mai guba a harin na Syria.

Kasashen duniya sun caccaki kazamin harin, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta lashi takobin gudanar da wani binciken kafin bayyana harin a matsayin laifukan yaki.

Gwamnatin Syria ta musanta kai farmakin yayin da aminiyarta Rasha ta dora laifin kisan kan ‘yan tawayen kasar.

Sai dai ’yan tawayen sun musanta ikirarin na Rasha.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.