Pakistan
Kungiyar ISIS ta kai hari ayarin motocin Mukaddashin Shugaban Majalisar Pakistan da Kashe mutane 27
Mayakan kungiyar IS masu ikirarin jihadi sun dauki alhakin wani kazamin hari na bam da aka kaiwa ayarin motocin mukaddashin shugaban majalisar Dattawan kasar Pakistan inda nan take aka kashe mutane 27.
Wallafawa ranar:
Talla
Majiyoyin samun labarai na cewa wani dan kungiyar IS dauke da jigidan bama-bamai ne ya kai harin kusa da garin Mastung mai tazaran kilomita 50 da birnin Quetta.
Mukaddashin Shugaban majalisar Dattijan Abdul Ghafoor ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an so kashe shi ne, Allah bai nufa ba, duk da haka ya sami raunuka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu