Isa ga babban shafi
IMF

IMF ta gargadi G20

Hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF ta yi gargadi ga manyan kasashe 20 masu karfin tattalin arzikin duniya G20 a game da wasu manufofi da ta ke ganin na barazana ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Shugaban Hukumar IMF Christine Lagarde
Shugaban Hukumar IMF Christine Lagarde REUTERS/Hannibal Hanschke
Talla

IMF ta yi wannan gargadin ne kafin taron kasashen na G20 da za a gudanar a ranar juma’a a Hamburg na Jamus.

Shugabar Hukumar Christine Lagarde ce ta yi gargadin a wani rahoton da aka ce ta shriya domin taron kungiyar G20 da za a gudanar a karshen makon nan mai zuwa a Hamburg na Jamus.

Largarde ta ce duk da cewa an samu ci gaba a tattalin arziki akwai bukatar manyan kasashen su gaggauta daukar matakai da karfafa kwarin guiwa ga kokarin farfado da tattalin arzikin duniya.

Lagarde ta yi kira ga kasashen G20 su dauki matakai a kan manyan basukan da ake binsu musamman China.

Sannan da shirin ta kwana game da rashin tabbas ga sabbin tsare-tsaren da Donald Trump na Amurka ke dauka kan tattalin arzikin Amurka.

Lagarde ta tabo batun daukar matakan da suka dace ga yawan jama’a da ke karuwa, musamman ta hanyar samar da ayyukan yi. Wanda zai haifar da Samun yawaitar kudade da inganta rayuwar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.